Kungiyar SERAP me fafutukar yaki da cin hanci da kuma kare hankin bil’adama ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari mako guda yayi bincike akan hadda akayi naira tiriliyan 11 ta wutar lantarkin Najeriya ta sulwanta.
Inda kungiyar ta bukaci Muhammadu Buhari daya umarci ministan Shari’a Abubakar Malami da sauran jami’an dake yaki da cin hanci da suyi bincike akan yadda aka yi da kudaden tun daga shekarar 1999.
Kuma ta kara da cewa idan ba’a dauki matakai bato nan da shekaru goma za’a iya yin asarar naira tiriliyan 20.