fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Kungiyoyin kwallon kafa na Premier League sun fara ragewa ‘yan wasansu Albashi

Hukumar professional Footballers Association ta kira wani taron gaggawa ga yan premier lig da EFL don su tattauna akan yadda coronavirus take tasiri a harkar wasannin kwallon kafa.

kulob Birmingham city sune suka fara sanar da yan wasan su cewa zasu rage masu albashi a ranar talata.
Hukumar PFA tace in har ana so a magance wannan matsalar to yakama ta kira taron gaggawa don su tattauna akan yadda zasu cigaba da tafiyar da al’amuran su.
Kulob din Birmingham city suna samun sama da euros 6,000 a sati amma yanzu an umurce su da  suyi hakuri su karbi kashi 50 bisa dari nadaga albashin su har na tsawon watanni 4.
Hukumar EFL ta sanar cewa zata ba kungiyoyin kwallon kafa taimakon euros miliyan 50 na gajeran lokaci.
 Kungiyoyin kwallon kafa da dama a nahiyar turai sun amice da tsarin rage albashin da kulob suke yi, wanda suka hada da Bayern Munich, Dortmund da dai sauran su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *