fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Kusan dala Biliyan 1 ce Abacaha ya sata>>Shugaba Buhari

Shigaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kusan Dala Biliya  1 ce tsohon shugaban kasa,Marigayi, Janar Sani Abacha ya sata daga shekarar 1993 zuwa 1998.

 

A bayanin da shugaban kasar yayi cikin wata jaridar kasar Amurka me suna Newsweek shugaba Buhari ya godewa kasashen Duniya da suka dawowa da Najeriya kudaden.

Duk da dai bai kira sunan Abacha ba a cikin jawabin, Hutudole ya fahimci cewa da tsohon shugaban kasar shugaba Buhari yake kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito.

 

Shugaba Buhari a lokacin mulkin Sani Abacha shine ya rike hukumar PTF.

 

Shugaba Buhari ya bayyana cewa a yanzu Najeriya zata iya ci gaba da ayyukan raya kasa da dama saboda kudin da aka dawo mata dasu kusan Dala Biliyan 1 wanda aka sace a mulkin soja na shekarun 90’s wanda kasashen Amurka, Ingila da Switzerland suka dawowa da Najeriya su.

Karanta wannan  Yadda hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad ya cigaba da karbar albashin miliyoyin naira duk da yayi murabus

 

Yace dawo da kudin ya nuna cewa kasashen Duniya a yanzu sun yadda da mulkin da ake a kasar na amfanae da mutane da ma sauran kasahen Africa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.