fbpx
Monday, August 3
Shadow

Kusan za’a iya cewa Shugaba Buhari ya gama da matsalar Boko Haram in banda abinda ba za’a rasa ba>>Mamman Daura

Dan uwan shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  Mamman Daura ya bayyana cewa kusan za’a iya cewa shugaba Buhari ya gama da matsalar tattalin Arziki in banda abinda ba za’a rasa ba.

 

Ya bayyana hakane a hirarsa da BBChausa yayin da yake magana akan harkar tsaro. Yace shugaban ya iske kusan kananan hukumomi 18 a hannun Boko Haram amma a yanzu duk an kwatosu.

Yace matsalar da ake fama da ita yanzu, sabuwar matsala ce.

 

Ga bayanin da BBChausa ta samo daga Baki Mamman Daura akan tsaro a hirar da ta yi dashi:

Malam Daura ya ce lokacin da gwamnatin Buhari ta zo akwai ƙananan hukumomi 18 na jihohin arewa maso gabashin Najeriya da ƙungiyar Boko Haram ta kafa tutocinta, inda suka kori sarakunan da ke yankin, ya ce a halin yanzu an yi maganin wannan kuma kusan an gama da su.

“Halin da ake ciki a yanzu sabuwar masifa ce, domin lokacin da aka kashe Shugaban Libiya Mu’ammar Gaddafi, sai gwamnatin ƙasar ta tarwatse, ya sayi ɗumbin makamai, duk sai aka yi ta wasoso, to shi ne duka (irin waɗannan) mutanen suke zuwa.

Najeriya da Mali da Burkina Faso da Chad da Nijar duk a hargitse suke,” in ji shi.

“Kuna zaune kawai a cikin ƙauye sai mutane su zo da babur su kashe na kashewa su ƙone na ƙonewa su ɓace.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *