fbpx
Friday, July 1
Shadow

Kuskure Ne Yi Wa Ƙaddarar Wani Dariya!

Kuskure Ne Yi Wa Ƙaddarar Wani Dariya!

A duk lokacin da shaiɗan yayi galaba akan mutum ko kuma mutum ya biyewa sharrin zuciyarsa har ta kai shi ga aikata ba dai-dai ba, to a lokacin yana buƙatar a nausar da shi tare da nuna masa illar Kuskuren daya aikata ba kyara da tsangwama ba.

A shekarar da akaci amanar Safara’u ta shirin kwana casa’in shine shekarar da lalacewarta ta zama mafari na lalacewar rayuwarta baƙi daya.

Nace cin amana domin kuwa ba video tayi ana iskanci da ita ba, yadda ta yi da wani ta tura masa video’s ɗinta tsirara shi kuma yaci amanarta ya bayyana su a duniya domin tozartata wanda hakan shine mafarin tarwatsewar rayuwarta.

Eh tabbas tayi kuskure domin yin video’s tsirara tare da turawa mutane kuskure ne ko ba’a faɗawa mutum ba, amma kowanne ɗan adam yana iya yin kuskure kuma hankali ake sanyawa a gyara ɓarna ba ɓarna da ɓarna ake gyara ba.

Ta fuskanci tsangwama kuma har aka cireta daga shirin kwana casa’in saboda abinda ta aikata wanda kamata yayi a zaunar da ita a nuna mata Kuskuren abinda tayi a kuma nuna mata illar hakan a kuma tausashi zuciyarta da irin kallon da wasu zasu rinƙa mata sai tayi haƙuri amma sai ya zama duk anrasa wannan daga ɓangarorin da suke mu’amala da ita.

Karanta wannan  Yankin Arewa maso yamma na APC yace shi za'a ba mukamin mataimakin shugaban kasa na Tinubu

Ita pha mace zuciyarta mai rauni ce kuma wani namijin wallahi shaiɗani ne hatsabibi ne domin gashi yayi silar tarwatsewar rayuwar yarinya da ƙarancin shekarunta har kyarar da ake mata ta sanya iskancinta ya tumbatsa bata shakkar kowa tun tanayi a ɓoye yanzu ta fito bata jin kunyar kowa.

Cikin masu mata dariya da ƙaddarar ta a rayuwa wasu iskancin da suke yi daga mazan har matan wallahi kare ma ba zai iya ci ba, amma muna take laifinmu muna hango nata har muna mata izgili da cin mutumci.

Zai fi kyau ace zaunar da ita akayi aka nuna mata illar halin da take son jefa rayuwarta da kuma makomarta a matsayinta na musulma hakan zaifi dacewa maimakon tozartata da muke tayi ba dare ba rana.

Allah ya tsare mu da mummunar ƙaddara a rayuwarmu baki daya Ameen Ya Hayyu Yaa Qayyum 🤲.

Ra’ayin Comr Haidar Hasheem Kano

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.