Wata Babbar Kotun Tarayya da ke da zamanta a jihar Kano ta sanya ranar 10 ga watan Disamba a matsayin ranar da zata yanke hukunci a kan zargin da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta gabatar a gaban kotu kan zargin badakar kudi harkimanin Naira Miliyan 950 da take wa tsohon ministan harkokin kasashen waje Aminu Wali da tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Mansur Ahmed.
EFCC ta zarge su da karbar kudi Naira miliyan N950 daga hannun jam’iyyar PDP a matsayin kudin yakin neman zabe a shekarar 2015, lamarin da hukumar EFCC ta ce ya saba wa tanadin doka.
Ya zuwa yanzu kotu ta ajiye ranar 10 ga watananan domin yanke hukunci.