fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Kuyi amfani da manyan makamai wajen yakar Fulani makiyaya.— Nnamdi Kanu ya gayawa Amotekun

Shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, Nnamdi Kanu, ya shawarci kungiyar tsaro ta Yammacin Najeriya, da aka sanya wa suna Amotekun, da su yi amfani da manyan makamai wajen yakar Fulani makiyaya.

Kanu ya fadi haka ne a ranar Juma’a yayin da yake maida martani ga kalaman Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed cewa makiyaya suna dauke da AK-47 ne saboda su kare kansu daga barayin shanu.

Kanu ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa “An Siyasantar Rundunar Tsaro Ta Amotekun.

Ya kara da cewa abin kunya ne ace Amotekun suna amfani da bindigogin gargajiya wajen tunkarar fulani makiyaya masu dauke da muggan makamai ciki har da AK-47, a dazuka masu matukar hadari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *