Me shirya fina-finan Hausa kuma jarumi, Amimu S. Bono ya saka wannan hoton a dandalinshi na sada zumunuta da yake nuna wani sashi na yawan mutanen da suka tarbi shugaban kasa, Muhammadu Buhari a yau, a garin Kano da kuma wani sashi na yanda mutanen Kanon suka tarbi shugaban kasa, lokacin da yaje yana yakin neman zabe.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Hoton dai ya nuna banbancin yawan mutane sosai sannan kuma Aminu S. Bono ya rubuta a jikin hoton kamar haka:
“
Akwai fa matsala, hoto na sama zuwan Buhari a yau tare da ‘yan gandujiyya, hoto na kasa zuwansa neman kuri’a tare da kwankwasawa, ayi gyara fa kwankwasonnan fa kanawa Tam….”
Tun bayan saka wannan hoto nashi sai muhawara ta kaure wasu suna kiranshi da makiyin buhari, wasu kuma sun goyi bayanshi, yayain da wasu sukace mutane sun dawo rakiyar Shugaba Buharinne shiyasa ba’amai tarba irin ta wancan lokacinba, amma wasu sunce ai taron yakin nemanzabe daban dana zuwa bude aiki.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Gadai wasu daga cikin irin muhawarorin da akayi akan wannan batu:
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});