fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Kwallayen Lewandowski na gasar Bundlesliga sun cika 30 a jiya

A jiya sati 6 ga watan yuni Robert Lewandowski yayi nasarar cin kwallon shi ta 30 a gasar Bundlesliga yayin da suka kara da Bayer Leverkusen, kuma Munich sun yi nasara a wasan wanda suka tashi 4-2.

Lucas Alario ya tsorata kungiyar Munich yayin daya zira kwallo a minti 10 na farko a wasan, tun daga nan kuma Bayern Munich suka fara yin kokari sosai kuma suka yi nasarar jefa kwallaye guda 3 kafin aje hutun rabin lokaci.
Lewandowski yayi nasarar cin kwallon shi ta 30 bayan an dawo daga hutun rabin lokacin, yan wasan Bayern Munich sun yi zanga zangar mutuwar George Floyd yayin da suka sanya wani abun ado na hannu wanda aka rubuta ” Rayuwar bakin fata “.
George Floyd ya kasance bakar fata kuma ya mutu ne a hannun wani dan sanda a garin Minneapolis dake kasar Amurka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.