Kwamandan Boko Haram me suna Malam Isah da wasu yaransa 4 sun tuba sun mika makamansu ga jami’an tsaron Najariya.
Ranar Juma’a data gabata ne suka mika kansu ga sojoji a Valley Shuwa dake jihar Borno, kamar yanda Zagazola Makama ya bayyana.
Mata 29 da kuma yara ne suka biyo bayan kwamandojin Boko Haram din suma suka mika wuya bayan ganin cewa ba’a kashe mazajen da suka mika wuya ba.
Jami’in sojin Najariya, Christopher Musa ya bayyana cewa jimillar ‘yan Boko Haram 67,000 ne suka tuba suka mika wuya ga jami’an tsaro.