Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu na Jihar Filato, Abe Aku ya harbu da cutar coronavirus.
Gwamnan jihar, Simon Lalong ne ya sanar da hakan ta hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Dan Manjang, a Jos, babban birnin jihar.
A sakamakon haka, Gwamna Lalong ya umarci dukkan membobin Majalisar zartarwar Jihar da su yi gwajin kwayar cutar corona sannan daga nan ya umarci su da su kebe kansu daga ranar 1 ga watan Yulin 2020.
Hakan ya biyo bayan da aka samu daya daga cikin mamban majalisar zartarwa kuma kwamishin kasuwanci da masana’antu Abe Aku da kamuwa da cutar biyo bayan gwajin da akai masa game da cutar Covid-19.
Dan haka bisa umarnin gwamnan an dauki samfuran kwamishinoni inda aka aike su zuwa cibiyar yin gwajin cutar, domin tabbatar da sakamakon nasu.