fbpx
Monday, August 15
Shadow

Kwamishinan addini na jihar Zamfara ya hada taron Sallah don a roki Allah ya kawo karshen matsalar tsaro

Kwamishinan addini na jihar Zamfara, Sheik Sani Tukur Jengebe ya hada gagarumin taron Sallah don a roki Allah ya kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Jengebe ya bayyana hakan ne a wani taron addu’a na musamman da aka gudanar a jihar domin a roki Allah ya kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya bakidaya.

Inda yace jihar Zamfara jiha ce dake da albarkacin noma sosai amma yanzu ta koma rokar abinci, hakan na matukar bata masa rai.

Saboda haka ya nemi shuwagabannin jihar kama daga sarakuna zuwa masu anguwanni cewa su gudanar da taron Sallah domin a roki Allah ya kawo masu dauki kan ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published.