Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo, CP Abutu Yaro ya bayar da umarnin kama wasu jami’an rundunar ‘yan sandan Edo hudu tare da tsare wasu ma’aurata bisa zarginsu da hannu wajen kashe wani dan banga mai suna Ikponwonsa Aikpitanyi a titin Obaze dake kan titin Ewah a cikin garin Benin, babban birnin jihar.
Jami’an da aka kama su ne Inspr. Igere Victor, Sgt. Umhenin Stanley, Sgt. Okongor Ojong da Cpl. Monday Joel yayin da ma’auratan da aka kama an bayyana sunayensu da Mista & Mrs. Sunday Egboh.
Kwamishinan ya ce rundunar da ke karkashin sa ba za ta lamunci ayyukan rashin da’a da ke da illa ga zaman lafiya da tsaron al’ummar jihar Edo.
Ya kuma ce za’a gurfanar da dukkan masu hannu a wannan danyen aikin a gaban kotu bayan an kammala bincike.