fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Kwamitin Dakile ya duwar cutar Korona dake jihar Kano ya raba kayayyakin kariya ga Kananan hukumomi 44 na jihar

Kwamitin yaki da cutar mai saurin yaduwa wato Coronavirus na jihar Kano ya rarraba kayayyakin kariya zuwa ga kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano domin dakile yaduwar cutar a fadin jihar.

Shugaban kwamitin na jihar Tijjani Hussain shine ya bayyana hakan, inda ya shaida da cewa manufar samar da kayyakin shine saukakawa tare da dakile yaduwar cutar daga matakin kananan hukumomin jihar.

Idan zaku tuna Jihar Kano na jerin Jahohin da cutar Coronavirus tai kamari duk da cewa ana samu cigaba sosai wajan yaki da cutar tun daga matakin jaha da kuma kasa baki daya.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *