Kwamitin mutane bakwai da gwamnatin jihar Zamfara ta kafa don bincike akan nadin sarauyar da aka yiwa kasurgumin dan bindiga ta bukaci a bata naira miliyan 3.2 don gudanar da ayyuka.
Kwanan nan sarkin Yandoto Aliyu Marafa ya nada Alero a matsayin shugaban Fulani wanda hakan yasa aka dakatar sa sarkin domin Aleru har yanzu hukuma na nemansa.
Kuma gwamnatin jihar Zamfara har kwamiti ta hada don bincike akan dalilin daya sanya aka bashi wannan sarautar bayan hukuma har naira miliyan biyar tasa kan duk wanda ya kamo shi.
Kuma kwamitin yanzu ta cewa gwamnatin jihar ta bata naira miliyan 3.2 don su gudanar da ayyukan nasu.