fbpx
Friday, December 2
Shadow

Kwana daya bayan amincewa da auren jinsi, bala’in mummunar ambaliyar ruwa ya afkawa kasar Cuba

A jiyane shafin hutudole.com ya kawo muku rahoto kan yanda mutanen kasar Cuba suka yi zaben raba gardama kan amincewa da auren jinsi ko kuwa akasin haka.

 

Sakamakon zaben ya nuna cewa, mafi yawancin ‘yan kasar sun amince da a halatta auren jinsi tsakanin ‘yan madigo da Luwadi.

 

Saidai kasa da wanni 48 da faruwar hakan, sai ga ambaliyar ruwa me tafe da mahaukaciyar guguwa da aka wa lakabi da Hurricane Ian ta afkawa kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, an dauke wuta a kasar saboda barnar guguwar sannan kuma mutane da dama sun rasa muhallansu.

 

Da farko dai mutane miliyan 1 ne matsalar wutar ta shafa, a yayin da ake kokarin dawo musu da ita, sai kuma wutar kasar gaba daya ta dauke inda mutanen kasar Miliyan 11 suka afka cikin duhu.

 

Kasar Cuba dake gaba a Duniya wajan noman taba, hakanan rahotanni sun bayyana cewa, ambaliyar ruwan ta daidaita yankin da ake noman taban.

Karanta wannan  An buƙaci masallatai da coci-coci su rage hargowa cikin dare

Zuwa yanzu dai mahukunta a kasar sun bayyana cewa, basu kai ga sanin irin barnar da ambaliyar ruwan ta yi ba.

 

An dai kwashe mutane da dama daga yankin da Ambaliyar ruwan tafi kamari, saidai har zuwa yanzu babu rahoton cewa wani ya mutu.

 

Tuni shugaban kasar, Miguel Díaz-Canel ya garzaya yankin da lamarin ya faru.

 

Yace zasu dauki matakin kare kayan amfanin gonarsu, musamman gonakin taba da sune kasar tayi suna dasu a Duniya.

 

Saidai masana sunce akwai yiyuwar karfin guguwar zai karu sosai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *