fbpx
Monday, August 15
Shadow

Kwanan nan ‘yan bindiga zasu yi garkuwa da shugaba Buhari, cewar Buba Galadima

Tsohon shugaban jam’iyyar APC Buba Galadima ya bayyana cewa kwanan nan ‘yan bindiga zasu yi garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Galadima ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na BBC Hausa inda ya bayyana masu cewa matsalar tsaro kara tabarbarewa kawai take yi a kullum.

Sbugaban jam’iyyar NNPP ya kara da cewa yanayin matsalar tsaron da ake a Najeriya ta nuna cewa shugaba Buhari ba zai taba iya yin komai akai ba, kuma ba zai magance matsalar ba.

Karanta wannan  Ya kamata gwamnoni su rika yin murabus daga shekara hamsin, cewar kungiyar kwadago ta kasa

A karshe yace harin da aka kaiwa gidan Kukukun Kuje ya nuna cewa shi kanshi Buhari bai tsira ba za a iya yin garkuwa dashi, kuma dama ‘yan bindigar sunce zasu yi garkuwa da shugaban kasar tare da gwamnan Kadum, El Rufa’i.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.