Shararren darekta kuma marubuci a masana’antar fina-finan hausa na Kannywood, Amiru Saira ya bayyana cewa kwanan nan zasu cigaba da haskaka shirin Labarina.
Kamfanin Amiru Saira ne ke shirya fim din wanda ake haskawa a tashar Arewa 24 a kowane mako.
Kuma ya bayyana hakan ne bayan da wani ya tambayesa yaushe zasu cigaba da haska fim din a Twitter, sai yace masa kwanan nan zasu cigaba sun kan aike ne.