Sansanin Peter Obi sun bayyana cewa dan takarar jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso so yake yayi amfani da farin jinin Obi don ya lashe zabe.
Doyin Okupe ne ya bayyana hakan yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels.
Inda yace masu maganar maja tsakanin NNPP Labour Party babu ita yanzu don ta mutu murus makonni hudu da suka gabata.
Inda ya kara da cewa maganar ta mutu ne tun bayan da wakilan Kwankwaso suka ce babu laifi idan wani dan Arewa ya sake yin mulki bayan shugaba Buhari.