Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shirya bayyanawa magoya bayansa aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Kwankwaso yace bayan kammala tuntuba kan aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa, ya shirya tsaf da bayyana hakan a mako me zuwa.
Kwankwaso yace duk wadanda ya tuntuba sun bashi karfin gwiwar ya fito takarar shugabancin Najeriya.