Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa kwankwaso ya bayyana cewa zasu yi maja da Labour Party a zaben 2023.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar asabar yayin da yake ganawa da BBC hausa, kuma ya tabbatar da cewa suna cigaba da tattaunawa da Obi da sauran membobin LP.
Haduwar Kwankwaso da Obi a jam’iyya guda ka iya basu nasarar lashe zaben shekarar 2023 kuma su kayar da PDP da APC wanda sula kasance fitattun jam’iyyun Najeriya.