fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Kwankwaso zan zaba ba zan goyi bayan Tinubu da Atiku ba domin ba zasu taimakawa Najeriya da komai ba, cewar tsohon mataimakin kansilan ABU

Shugaban kungiyar dattawan Arewa, farfesa Abdullahi Ango ya bayyana cewa mayan ‘yan takarar dake neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa ba zasu iya magance matsalolin kasar ba.

Inda yace dan takarar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar ba zasu taimakawa Najeriya da komai domin sun dade a karagar mulkin amma ba abinda sukayi.

Inda yace gwara dan takarar jam’iyyar NNPP tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso da mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo wanda ya fafi zaben fidda gwani a APC.

Karanta wannan  Yadda mutane kusan miliyan guda suka mamaye jihar Nasarawa domin nuna goyon bayansu ga Peter Obi

Tsohon mataimakin kansilan jami’ar ABU ta Zaria ya kara da cewa Peter Obi ma duk ya fi Tinubu da Atiku, saboda haka ba zai goyi bayan kowa a cikinsu ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.