fbpx
Friday, July 1
Shadow

Kwara ka zuba kudinka a harkar Fim da ka gina Islamiyyu da Masallatai>>Aminu sharif Momo

Fitaccen Jarumi a Masana’artar Kannywood kuma mai gabatar da shirin kundin Kannywod da Sharhin Finafinan Hausa a tashar Arewa24 Aminu Sharif Momo ya ce sadakatu jjariya ce mai karfi matukar masu halinmu su ka bada kudade don a shirya masu shirya Fina-Finan Hausa,

 

Ya ce Ya ce a yanayin da ake ciki yanzu da a gina masallatai da islamiyyu gwara a zuba kudaden a harkar shirya fina-finan hausa.

 

Aminu Sharif ya bayyana hakan ne cikin shirn ‘Barka da hantsi’ na gidan rediyo freedom a jiya Laraba.

 

Ya ce zuba kudaden a masana’antar ta kanywood sadaka ce mai gudana da za a amfana ana duniya da gobe kiyama.

 

Momo ya kuma yi kira ga mawadata da su dinka tallafawa masana’antar ta Kannywood da kudade kamar yadda suke tallafawa marayu da sauran masu bukata ta musamman.

Karanta wannan  Kalli bidiyon yanda wani Bahaushe ke Inyamuranci kai kace sunansa Chinedu

 

Ya kuma ce duk wanda ya zuba kudinsa a harkar fim tamkar yayi sadakatul jariya ne don kuwa ladan zai bishi har zuwa kabarinsa matukar za a dauka a kalla to zai samu lada a cewar sa.

 

Ya ce ai kamar yadda zaka tattara kudi akai hukumar zakka ko akai tallafi gidan mabukata ko asabita gara ka zuba jarin a fim din Hausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.