Wata Babbar kotun tarayya dake jihar Kwara ta yanke wa wani matashi mai shekaru 34 mai suna Kelvin Monye, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda kamashi da laifin damfara.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ita ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Tweeter a ranar Litinin.
A cewar hukumar bayan samun mai lafin na da hannu dumu-dumu a dafarar wasu kudade tuni Al’kalin kotun, Mahmood Abdulgafar, ya umarci da a tisa keyar mai laifin zuwa gidan gyara domin girbar laifin da ya aikata.