Kyakkyawan Shugabanci: NLC Ta Yabawa Gwamna Inuwa, Tare Da Alkawarin Nema Masa Ƙuri’u Gabanin Zaben 2023
…Yayin Da Gwamnan Ya Yaba Da Kyakkyawar Alaƙar Dake Tsakanin Gwamnatin Sa Da Ƙungiyoyin Kwadago
…Ya Bada Kyautar Bus Mai Kujeru 18 Ga Kungiyar Ta NLC A Gombe Ɗin Sauƙaƙa Harkokin Ta.
Bayan sauraren jerin nasarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ta cimma a cikin shekaru 3 da rabi da ba a taba ganin irin su ba, ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen Jihar Gombe ta yi magana da murya guda cewa gwamnan ba kawai gagarumar nasara ya samu ba, ya ma cancanci goyon bayan ƙungiyar don ƙara nausa jihar gaba.
Hakan ya faru ne yayin wani taron tattaunawa da kwamitin siyasa na ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar ya shirya, ga ɗokacin ‘yan takaran jam’iyyun siyasa a Jihar Gombe.
Shugabannin ƙungiyar ta NLC wadanda da farko suka halarci bikin miƙa cek ɗin kuɗaɗen sallama ga ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar wadda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya miƙa, suka ce sun gamsu cewa gwamnan yana da kyawawan manufofi ga al’ummar Jihar Gombe, kuma ya cancanci samun goyon bayan ma’aikata.
A yayin bikin gabatar da cek ɗin, bayanai sun nuna cewa ya zuwa yanzu gwamnan ya biya bashin kimanin Naira biliyan 7 da miliyan 900 ga waɗanda suka yi ritaya a jihar, duk da cewa bashi ne da gwamnatin sa ta gada, amma duba da halin da talakawa ke ciki, Gwamna Inuwa ya biya, baya ga ƙarin girma ga ma’aikatan da suka jima a mataki guda tsawon shekaru.
Shugaban Kungiyar Kwadagon ta Najeriya wanda mataimakin sa Kwamared Bappayo Abdulmumini ya wakilta, ya bayyana cewa ayyukan Gwamna Inuwa Yahaya a fannin siyasa da shugabanci nagari sun sanya shi yin fice a shekaru uku da rabi da suka gabata.
Da yake bayyana amincewa da gwamnatin ta Inuwa Yahaya, shugaban ƙungiyar kwadagon yace, “Shugabannin mu na ƙasa ne suka umarce mu da mu tattauna da duk ‘yan takaran gwamna tare da rattaba hannu dasu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da miƙa shi ga uwar ƙungiyar ta kasa, amma mu a nan Jihar Gombe mun cimma matsaya cewa ba zamu rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kai ba, domin ƙungiyar mu tana sane da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin ka tun zuwan ka kan karagar mulki.”
Bisa la’akari da abin da ka yiwa ma’aikatan Jihar Gombe kawo yanzu; haɗe da wasu kyawawan manufofi da ayyukan da ka aiwatar, bamu da wani zaɓi daya wuce mu nema maka goyon baya. Ina sane da cewa ka ci zaɓe a 2019 da kuri’u fiye da dubu 300. A nan ƙungiyar kwadago, muna da mambobi fiye da dubu 60. Idan kowannen mu zai iya farauto kuri’u akalla biyar, hakan na nufin ƙungiyar kwadago kaɗai zata iya baka ƙuri’un daka samu a zaben daya gabata, kuma na tabbatar hakan zai baka nasara.”
Da yake jawabi yayin ganawar, Gwamna Inuwa Yahaya yace gwamnatin sa ta himmatu kwarai wajen aiwatar da manufofin da suka shafi jama’a, masu tasiri ga ayyukan gwamnati da ci gaban jama’a a jihar.
Ya kuma jaddada cewa yana nan kan manufofin sa na 2019 a cikin shekaru uku da rabi na shugabancin sa, kuma bayanai da alkaluma sun tabbatar da kwazon sa kamar yadda ya alkawarta yayin yaƙin neman zaɓen sa.
Gwamna Inuwa yace “Babu wani mai tunani hankali da zai kushe wannar gwamnatin idan aka yi la’akari da ayyukan raya kasa data gudanar a sassa daban-daban da suka haɗa da bunƙasa ayyukan gwamnati,”
Gwamna Inuwa Yahaya ya yaba da haɗin kai da kyakkyawar alaƙar dake tsakanin gwamnatin sa da ƙungiyoyin kwadago don ci gaba da gudanar da shugabanci nagari.
Shi yasa wannar gwamnatin take tafiyar da harkokin mulki a bayyane har ta kai ga bayyana muku haƙiƙanin yadda muke tafiyar da kuɗaɗen gwamnati don tabbatar da aminci da gaskiya da riƙon amana”.
Da yake ƙarin haske kan wasu manufofin sa daya gabatar a wurin taron, Gwamna Inuwa yace tattalin arziki shine tushen da duk sauran manufofi ke ta’allaƙa a kai, kuma tattalin arzikin Jihar Gombe ya ta’allaƙa ne kan noma saboda haka yawancin jama’ar mu ko dai manoma ne ko kuma makiyaya, shi yasa gwamnatin sa ta sake farfado da masana’antar sarrafa takin zamani a jihar.
Yace gwamnatin sa tana bada kulawa sosai ga manoman Jihar Gombe ta hanyar ware kuɗaɗe da taki da sauran harkokin tallafi.
“A yau, muna gina wata katafariyar cibiyar masana’antu ta biliyoyin naira a garin Daɗinkowa domin samar da ayyukan yi ga matasan mu, gwamnati ita kaɗai ba zata iya ɗaukar kowa aiki ba, amma tana iya samar da yanayi mai kyau ga kamfanoni masu zaman kansu su ci gaba, shi ya sa muke aiki tukuru don ganin an samu nasarar aiwatar da aikin cibiyar masana’antun”, in ji shi.
Gwamna Inuwa yace, “Wani babban ci gaba da gwamnatin sa ta samu shine na gina hanyoyi a faɗin jihar a ƙarƙashin shirin samar da hanyoyi kilomita 100-100 a kowace ƙaramar hukuma. Gwamnan ya buga misali da hanyar Degri zuwa Talasse dake Ƙaramar Hukumar Balanga wanda duk gwamnatocin da suka gabata suka kasa yi amma gwamnatin sa tayi iya bakin ƙoƙarin ta wajen inganta rayuwar al’umma da harkokin zamantakewa a yankin.
Yace ayyukan hanyoyi sun samar da ci gaba na zahiri a Jihar Gombe, duba da dimbin kilomitocin hanyoyin da aka gina a ƙananan hukumomin jihar.
Gwamnan yace idan aka ɗan yi waiwaye, ya inganta ayyukan gwamnati matuka, duba da irin halin da sashin ya tsinci kansa a yayin da ya karɓi ragamar mulki. Don haka ya gayyaci shugabannin ƙungiyar ta NLC su zagaya dukkan ƙananan hukumomin jihar su binciki duk abin da yace gwamnatin sa ta aiwatar.
Gwamna yace gwamnatin sa ta gaji bashin fiye da Naira biliyan 120 baya ga almubazzaranci da aka yi da kuɗaɗen ƙananan hukumomi, da rashin da’a a tsarin aikin gwamnati, lamarin daya haifar da ma’aikatan bogi da kuma gudanar da yarjejeniyoyin da basu dace ba amma gwamnatin sa ta ɗauki matakan gyara kura-kuran.
Ya koka da cewa, “Duk da tallafin da gwamnatin tarayya ta bayarda nufin kawar da matsalolin ma’aikata daga kuɗaɗen rarar mai da kuɗaɗen tallafi na Paris Club, da Bail Out da makamantan su, amma gwamnatin data shuɗe ta kasa biyan hakkokin ma’aikatan da suka yi ritaya.
Cikin jin daɗi gwamnan yace “Amma daga lokacin da muka hau mulki zuwa yau, mun biya kuɗaɗen sallama na ma’aikatan jiha na shekarar 2014, da 2015, da 2016 da kuma 2017, gashi a yau mun fara biyan ‘yan fanshon na jiha kuɗaɗen su na 2017”.
Ya ƙara da cewa “Gwamnatin mu ta kuma amince da ƙarin girma ga fiye da ma’aikatan ƙananan hukumomi dubu 26 waɗanda gwamnatocin da suka shuɗe suka yi watsi dasu.
A fannin kiwon lafiya, Gwamna Inuwa Yahaya yace baya ga tsarin taimakekeniyar lafiya na Jihar Gombe (Go-Health) da gwamnatin sa ta bullo da shi, gwamnatin ta inganta cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko a gundumomi 114 dake jihar da manyan asibitocin Bajoga da Kaltungo da aka inganta su, yayin da ake aikin gina sabon babban asibitin garin Kumo dake Ƙaramar Hukumar Akko.
Gwamna Inuwa yace ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin sa ta ɗauka dangane da matsalar rashin aikin yi shi ne ta fannin samar da muhimman ababen more rayuwa da suka haɗa da aikin cibiyar masana’antu na Muhammadu Buhari, irin sa na farko a tarihin jihar wanda aka tsara don ƙara bunƙasa ci gaban sauran sassan tattalin arziki; kamar ɓangaren noma, wanda zai ƙara karfafawa da bunƙasa tattalin arziki, zai kuma taimakawa manoma wajen samun damar shiga kasuwanni da samun kyakkyawan farashin da zai samar da ribar wahalhalun da manoman suka sha.
Da yake magana kan sirrin gagarumin nasarar da gwamnatin sa ta samu duk da ƙarancin kuɗi da kuma annobar Covid-19 data addabi duniya a baya-bayan nan, cikin zolaya, Gwamna Inuwa yace “ba wai bamu san daɗi ba ne, kuna ganin ba mu san yadda zamu tafi Dubai ko Amurka da London ba ne? A’a muna da kishin jama’a ne tare da bada fifiko ga harkokin su, kuma kuna daga cikin su, taka tsantsan din mu ne ya bamu damar biyan kuɗaɗen, ni akawu ne, kwararre ma kuwa ta wannan fannin kuma ɗan kasuwa; don haka na san yadda zamu amfana daga kuɗaɗen mu,” in ji shi.
A matsayin tukuici kan goyon baya ga haɗin kai da fahimtar juna da NLC, Gwamnan ya mikawa ƙungiyar mabuɗin motar bas mai ɗaukar mutane 18 kyauta don kara inganta ayyukan kungiyar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kasance a dakin taron kungiyar dake Labour House ne tare da Babban Daraktan Kwamitin Yakin Neman Zaɓen APC Barista Zubair Muhammad Umar, da Kwamishinoni, da jiga-jigan APC kamar Dr Bala Bello Tinka da dai sauran su.
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe