Ministan Sufurin, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa a kyauta kamfanin kasar China na CCECC zai gin jami’ar Sufuri ta Daura.
Ya bayyana hakane yayin da yaje ran gadin aikin a Daura inda yace alkawarin da aka yi shine ‘yan Chinar zasu kwashe shekaru 5 suna aiki a makarantar inda daga nanne kuma sai Najeriya ta karba.
Yace ana tsammanin shafe shekara 1 ana ginin Jami’ar kuma akwai makarantun sakandare dana Firame da za’a gina a cikin jami’ar saboda ma’aikatan da zasu je daga nesa.
Jami’ar dai za’a gina ta ne akan kudi Dalar Amurka Miliyan 50. Hutudole ya samo muku cewa ‘yan Najeriya da dama sun nun rashin jin dadinsu akan hakan inda suke cewa ya kamata a bincika dai kasar China ba zata yi komai a kyauta ba, akwai wani abu a kasa.