fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Kylian Mbappe ya rage daraja sosai a kasuwar yan wasa

Tauraron dan wasan Faransa na kungiyar PSG, Kylian Mbappe ya rage daraja a kasuwar yan wasa har na kimanin yuro miliyan 99 a cikin watanni bakwai kacal a cewar masu lura da farashin yan wasan tamola na CEIS.

A shekara data gabata cikin watan yuni, farashin Mbappe ya kasance yuro miliya 234 wanda hakan yasa ya kasance dan wasa mafi tsada a fadin duniya, amma yanzu a watan janairu na shekara ta 2021 farashin dan wasan ya koma yuro 135.

Yayin da farashin Mbappe ya ragu a kasuwar yan wasa cikin watanni 7, shi kuma farashin tauraron Manchester United Marcus Rashford ya hauhawa da kimanin yuro miliyan 12, wanda hakan yasa farashin dan wasan ya koma yuro miliyan 149 kuma ya zamo dan wasa mafi tsada a fadin duniya a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.