Monday, March 30
Shadow

Labarai masu dadin ji game da Cutar Covid-19

Cutar Covid-19 cuta ce da tazama babbar barazana ga duniya baki daya, wanda duniya a halin yanzu ke fama da yaki akanta domin dakile ya duwarta a fadin duniya.

Sai dai a wasu rahotanni na nuni da cewa an fara samun saukin cutar kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kamar yadda jaridar New York Post ta rawaito cewa kasar chaina ta rufe asbutocin wucin gadi wanda ke kula da masu cutar Covid-19 a yankin wuhan a sakamakon babu wanda aka Kara samu dauke da cutar ba.

Haka yake a jaridar Times of India ta rawaito cewa Likitoci a India sun yi nasarar ceto wani mara lafiya dan kasar Italiya da a ka samu dauke da cutar ta hanyar amfani da wasu magun guna, da suka hada da Lopinavir, Ritonavir da kuma Oseltamivir da Chloroquine.

Jaridar kasuwanci ta BBC ta rawaito cewa Kamfanin Apple ya sake bude shagonan sa guda 42 dake Chaina.

Dalilin da yasa kasar Italiya ke fustantar mummunan tasirin cutar a kasarta nada nasaba da yawan tsofafi dake dasu a kasar, wanda kasar ce ta farko mafi yawan tsofaffi a yankin turai baya ga kasar Japan a duniya, kamar yadda jaridar ABC NEWS da New York Times suka rawaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *