Wata majiya daga gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa BBC cewa labarin da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta na cire gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele, ƙarya ne.
A cewar majiyar, wacce ba ta so mu ambaci sunanta saboda ba ta samu izinin magana kan batun ba, Shugaba Buhari bai cire Mista Emefiele ba.
Jita-jitar ta fara ne a shafin tuwita.
Daga baya sai labarin ya yaɗu sosai inda aka ambaci maudu’in labari sau fiye da 12,000 a tuwitar cikin awa biyu.
Sannan wasu kafafen yaɗa labaran na intanet su a sun bi sahu wajen yin labarin.
CBNta mayar da martani
Wani mai magana da yawun CBN, Dr Abdulmumin Isa ya shaida wa BBC cewa shi ma tsintar labarin cire gwamnan babban bankin ya yi.
“Ban san komai a kan hakan ba. Mu ma a intent muka ga labarin, in ji shi.
A shekarar 2014 ne Godwin Emefiele ya zama gwamnan CBN 2014.