fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Labaran kasuwar kwallon kafa: Manchester United da Chelsea da Arsenal sun ziyarci kasuwar yan wasan domin su kara da Man City da kuma Liverpool a kakar wasa mai zuwa

Zakarun gasar premier league wato Liverpool suna harin siyan dan wasan baya na kungiyar Schalke Ozan Kabak, wanda kungiyar shi ta sa mai farashin euros miliyan 40. Da yiwuwar Schalke zasu siyar da shi kasa da wannan farashin saboda rashin kudi amma sai dai Liverpool suna da abokan hammaya wajen siyan shi kamar Man City, Juventus da Dortmund.

 

United suna tattaunawa da Dortmund akan Jadon Sancho, amma sai dai United sun rage kusan euros miliyan 10 zuwa 15 cikin farashin dan wasan na kusan euros miliyan 90. Saboda rashin kudin siyan Sancho, United suna harin siyan dan wasan Villa Grealish. An gayama Jack cewa ba dole ne ya samu buga wasa a kowane mako ba,amna wannan ba zai hana kaftin din Villa kokawa kungiyar da zata habaka mai sana’ar shi da kudaden shi ba.

 

Karanta wannan  Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United ne saboda Lionel Messi, karanta kaji dalili

Arsenal suna harin Coutinho wanda kwantirakin aron shi da Munich ya kare kuma Barcelona take shirin kara bayar da shi Aro. Amma babbar matsakar Arsenal shine Aubameyang ya amince da sabon kwatiraki yayin da Barcelona da Milan suke harin siyan shi. Mikel yana da burin siyan wasu yan wasa kamar Thomas Partey da Joelson da kuma Danilo Pereira.

 

Suma Chelsea sun shirya siyan dan wasan Leverkusen Kai Havertz yayin da suka fara tattaunawa da kungiyar akan dan wasan bayan sun tabbatar da cewa suna cikin gasar zakarun gasar nahiyar turai mai zuwa.Tsohon tauraron United Roy Kayne ya bukaci kungiyar data siya wani kwararren golan akan David De Gae idan har tana so ta lashe kofin premier lig.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.