fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Labaran kasuwar kwallon kafa: yayin da Haaland yayi jawabi shi kuma Ibrahimovic zai sabunta kwantirakin shi

Ana sa ran Chelsea zasu fara yin amfani da Willy Caballero a wasan da zasu buga ranar sati na FA Cup,kuma watakila Kepa Arrizabalaga ya buga wasan shi na karshe a kungiyar.Yayin da Sun suka bayyana cewa dan wasan yana ganin cewa kungiyar Chelsea tana dora gabadaya laifukan ta a kashi tunda Lampard ya fara jagorancin kungiyar. Lampard yana harin siyan Oblak ko Neuer ko Pope da dai sauran su. Domin ya maye gurbin Kepa.
Erling Haaland ya yayi jawabi akan cigaba da wasan shi a Dortmund, yayin daya bayyanawa Bild cewa yanada kwantiraki mai tsawo har 2024 a Dortmund,kuma burin shi shine lashe kofin gasa a kungiyar kuma yayi murna tare da masoyan kungiyar baki daya.
David Silva zai koma duk kungiyar da yake so a kyauta da zarar Man City sun kammala buga wasannin su na gasar zakarun nahiyar turai,yayin da Inter Miami, Valencia,Las Palmas, Sabab Al-Ahli da Al-Nasir ke harin siyan shi a cewar Daily Mail.
La Gazzetta Dello Sport sun bayyana cewa Zlatan Ibrahimovic zai sabunta kwantirakin shi a kungiyar AC Milan. Kuma kwantirakin shekara daya kacal zasu yi mai tare da zabin kara buga wani kakar wasa a kungiyar da karin albashi na euros miliyan hudu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan wasan Manchester sun bukaci a sayar da Ronaldo kuma har yanzu baya jituwa da sabon kocin kungiyar

Leave a Reply

Your email address will not be published.