fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Labaran kasuwar yan wasan kwallon kafa: Yayin da Chelsea ta shiga cikin kungiyoyin dake farautar siyan Erling Haaland

Kungiyar Chelsea ta shirya fafatawa da manyan kungiyoyin dake harin siyan tauraron dan wasan Dortmund, Erling Haaland yayin da Manchester United da City da Real Madrid da kuma Juventus duk suke cikin mashahuran kungiyoyin da suke harin siyan dan wasan.

Erling Haaland ya koma kungiyar Dortmund ne daga Salzburg a watan janairu, kuma yayi nasarar ciwa kungiyar kwallaye 33 a wasanni 32 daya buga mata tun komawar shi.

Manema labarai na Mirrow sun bayyana cewa siyan Haaland zai yiwa Manchester United wuya duba da yanayi alakar su da wakilin dan wasan Mino Riola, yayin da suka kara da cewa kungiyar zata mayar da hankulanta wurin siyan tauraron dan wasan Everton, Calvert Lewin.

Karanta wannan  Zamu sayar da kai amma bisa sharadi guda, Manchester United ta fadawa Cristiano Ronaldo

Kungiyar zakarun gasar Premier League ta Liverpool tana harin siyan dan wasan baya duba da yadda tawagar take shan gwagwarmaya ta bangaren baya yayin da Van Dijk da kuma Gomez suka samu raunika. Wasu daga cikin yan wasan da kungiyar ke hari sun hada da dan wasan baya na kungiyar Real Madrid Eder Militao acewar Tojofichajes, yayin da kuma take tattaunawa da Celta Vigo akan dan wasan ta Stefan mai shekaru 16.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.