Gwanin kasuwar kwallon kafa, Fabrizio Romano ya bayyana cewa kungiyar Chelsea ta taya tauraron dan wasan Manchester, Cristiano Ronaldo.
Kuma ya kara da cewa ta taya shine a farashin yuro miliyan 15 sannan alamu sun bayyana cewa Ronaldo zai amince ya cigaba da wasa a gasar ta Firimiya.
A ranar asabar Ronaldo ya cewa Manchester ta sayar da shi domin bata saya dan wasa ba a wannan kakar sannan kuma ba zata buga gasar zakarun nahiyar turai ba.