fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Labari Mai Dadi: Gwamnatin Borno ta rufe sansanoni yan gudun hijira tare da mayar da su gidajensu

Gwamnatin jihar Borno ta mayar da mutane sama da 20 da mayakan Boko Haram suka raba da gidajensu a jihar.

Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda mataimakin gwamnan, Hon. Umar Usman Kadafur ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Maiduguri a yayin mika tallafin kayayyakin abinci da gwamnatin tarayya ta bayar ta hannun ma’aikatar jin kai da magance bala’o’i da ci gaban al’umma.

Zulum ya godewa gwamnatin tarayya bisa wannan daukin, yana mai cewa “zaman lafiya da muke samu ne ya sa muka rufe wasu sansanin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri Metropolitan da karamar hukumar Jere.”

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

Ya kara da cewa “Sama da al’ummomi 20 ne aka sake tsugunar da su zuwa gidajen kakanninsu. Gwamnatin jihar Borno na tabbatar da cewa sun karfafawa dukkan al’ummomin da aka sake tsugunar da su gwiwa.”

Ya kuma tabbatar wa cewa gwamnatin jihar ta samar da hanyar da za ta bi domin ganin an yi rabon kayan abincin ba tare da wata matsala ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.