Ruwan wutar da sojojin Najeriya sukawa wata maboyar kungiyar Boko Haram ya kashe wani dan Boko Haram me suna Abu Fatima wanda kuma kwamandane a kungiyar.
Hakanan an kashe mayakansa 15, lamarin ya farune a kusa da tafkin Chadi.
Abu Fatima shine ya gaji tsohon shugaban kungiyar, Bakura RPG, da Adam Kaiga wanda duk an kashesu sanadiyyar hare-haren sojojin Najeriya.
Kwamandan na da mayaka akalla 500 dake amsar umarni daga gareshi wanda suke a gurare daban-daban na dajin Sambisa.
Kamin mutuwarsa, ya jagoranci kaiwa sojojin Najeriya hare-haren daban-daban.
Kokarin sojoji na gamawa da kungiyar gaba dayanta na kara samun nasara sosai, kamar yanda Zagazola ya ruwaito.