fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Labari me dadi: Gobe zamu janye yajin aiki, cewar ASUU

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta ASUU data kasance tana yajin aiki na kusan watanni hudu zuwaya biyar ta bayyana cewa zata janye yajin aikin nata.

Amma fa sai idan gwamnatin tarayya ta amince da bukatunta kuma ta rattaba hannu kamar yadda ta amince da bakinta.

Shugaban ASUU, Emmanuel Osodoke ne ya bayyanawa manema labarai na Channels hakan inda yace sun kammala yarjejeniya da gwamnati.

Kuma zasu iya janye yajin aikin gobe idan har gwamnatin ta amince da bukatunsu na biyansu da tsarin UTAS.

Karanta wannan  APC ta gaza domin shugaba Buhari bai damu da ilimin Najeriya ba, cewar daliban Najeriya

Amma abin tambaya shine yaushe gwamnatin zata amince ta kira su?.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.