Sojojin Najeriya na MNJTF wato Operation Gama Aiki da kuma sojojin Niger da Cameroon sun yi nasarar kashe kwamandojin yan Boko Haram guda 10 tare da ‘yan ta’addansu sama da 100.
Tawagar sojojin ta hada da sojojin kasa dana sama hadda Operation Yaki, inda suka hada kai suka budewa yan ta’addan wuta dake boye a Chadi.
In mai magana da yawun MNJTF, Muhammad Dole ya bayyama cewa sunyi nasararar bata masu muhallinsu kuma sun ceto mutane da suke tsarewa a mabuyar tasu.
Amma abin bakin ciki shine jami’ai 18 sun samu rauni hadda kwamanda yayin da kuma wasu guda uku suka rasa rayukansu.