fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Watakila Neymar zai maye gurbin Ronaldo a Madrid: Baban Neymar din ya gana da me kulub din Real Madrid akan wannan batun

Rahotanni daga jaridar The Sun ta kasar Ingila sun bayyana cewa mahaifin dan wasan kwallon kafa da yafi kowane tsada a Duniya Neymar da yanzu haka yake bugawa kungiyar kwallon kafa ta PSG wasa, ya gana da me kulub din kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez akan yiyuwar maye gurbin Cristiano Ronaldo da danshi Neymar.


A shekarar 2021 ne idan Allah ya kaimu kwantirakin Cristiano Ronaldo da ya sawa hannu na bugawa Real Madrid din wasa zai kare, shine baban Neymar din yake so ya kama kafa dan ganin danshi ya maye gurbin Ronaldon.

Shi dai Neymar wanda ya koma PSG daga Barcelona akan makudan kudi da suka kai sama da fam miliyan dari biyu wanda hakan yasa ya zama dan kwallo mafi tsada a Duniya, an ruwaito wasu tsegumi dake cewa dan wasan baya jin dadin zama a PSG din, amma irin yanda yake rayuwa da zagayawa a gari bai nuna rashin jin dadi ba tattare dashi. 

Karanta wannan  Sanata Binani Ta Yi Maza Zarra, Inda Ta Lashe Zaben Fidda Gwani Na Gwamnan Adamawa A Karkashin Jam’iyyar APC
Hoton Neymar da babanshi
Haka kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa su kansu Kulub din na PSG na dari-darin kar idan Neymar din bai samu yin wani katabus ba a gasar Faransa zai iya ya nemi barin kulub din wanda kamar yanda rahotannin suka bayyana, hakan yasa ake kula dashi sosai yanda ya kamata. 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.