fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Labarin Wasanni: AFCON: Kocin Algeria ya caccaki ‘yan jaridar Najeriya

A ganawa da manema labarai da me horas da ‘yan kungiyar kwallon kafar kasar Algeria, Djamel Belmadi yayi ta kamin fara wasa ya caccaki ‘yan Jaridar Najeriya bayan wata tambaya da aka mai da bata mai dadi ba.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wata ‘yar jaridan Najeriya me suna, Chisom Mbonu-Ezeoke ce ta tambayi kocin ko me zaice akan abinda ya faru a wasan da kasar Algeria ta buga da Kwadebuwa inda dan wasanshi na baya, Sofiane Feghouli ya makala hannunshi a jikin Wilfred Zaha ya fadi da gangan yana jiran alkalin wasan ya hura mai mugunta, abinda ya dauki hankula sosai.
Kocin yaki amsa tambayar inda yace ‘yar jaridar ta Najeriya bata san aikin ta ba, amsar daya bayar tasa ‘yan jaridar Algeria dake gurin suka tafamai a matsayin yabawa da amsar tashi, nan sai dakin tattaunawar ya kacame da cece-kuce inda sai da wanda ya shirya wannan tattaunawa, Ibrahim Sani dan kasar Ghana ya jawo hankalin ‘yan jaridar da cewa su kulafa su ‘yan jaridane ba magoya bayan wani mutum ba, tafin da aka yi be kamataba.
Hakanam shima kocin Najeriya, Gernot Rohr da aka tambayeshi akan irin matakin da yake shirin dauka akan irin wannan dabi’a ta ‘yan wasan Algeria ta neman huri da gangan cewa yayi, abonda ya sani shine FIFA bata yadda da irin wannan abuba dan haka zasu bauwa Rafali wannan aikin, shi abinda ke gabanshi yanazu shine shirin tunkarar kasar.

Karanta wannan  Kalidou Koulibaly da Raheem Sterling sun bugawa Chelsea wasan Premier league na farko da kafar dama

Shima dan wasan Najeriya, Kenneth Omeruoya bayyana cewa kocin su ya basu umarnin kiyaye taba dan wasa a guraren dake da hadari sannan kuma yace zasu yi kokarin ganin sun gujewa duk wata yaudarar ‘yan wasan na Algeria da suke amfani da ita a wasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.