fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Labarin Wasanni: Ana cece-kuce tsakanin kocin Najeriya dana Afrika ta kudu: Abubuwan da ya kamata kasani game da wasan

A gobe, Laraba ne da misalin karfe 8 na yamma idan Allah ya kaimu ‘yan kwallon Najeriya, Super Eagles zasu hadu da ‘yan kwallon kasar Afrika ta kudu,Bafana-Bafana a wasan kusa dana kusa dana karshe a ci gaba da gasar neman daukar kofin nahiyar Afrika, kamar yanda yake a cikin labarin wasanni.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Labarin wasannin dake ci gaba da bayyana akan wasannin na gobe sun bayyana cewa an yi hirar kamin wasa da wakilan kungiyoyin biyu da zasu kece raini gobe inda Kocin Najeriya, Gernot Rohr ya bayyana ‘yan kwallon Bafana-Bafana na South Afrika a matsayin wanda aka fiso bayan da suka cire me masaukin Baki, Egypt daga gasar a zagayen kashe 16 da aka kammala.
Ya kuma kara da cewa, duk ‘yan wasanshi 23 a yanzu a shirye suke su buga wasa, ba kamar yanda aka fara gasar ba inda ya samu matsalar zabar ‘yan wasan da zai fara wasa dasu, hakan na nufin ‘yan kwallon irinsu Mikel Obi, Shehu Abdullahi, da Jamilu Collins duk sun warke daga ciwukan da suka ji.
Rohr ya kuma ce a garin Cairo inda za’a yi wasan na gobe akwai zafi dan haka sai sun jure.
Hakanan labarin wasannin na yau sun bayyana cewa shugaban hukumar wasanni ta kasa, NFF watau Amaju Pinnick ya bukaci ‘yan kwallon da su sakawa shugaban kasa,Muhammadu Buhari da kowane irin taimako na kudi da goyon baya ya bayar ta hanyar cin kasar Afrika ta kudu gobe da kuma daukar kofin na AfCON.
Labarin wasanni ta bangaren kasar Afrika ta kudu shima na cewa kocin kungiyar, Staurt Baxter wasa daya kawai ba zai sa su zama wanda aka fi so a gasar ba kuma kocin Najeriya kar yayi tunanin zai musu wayaune.
Daga bangaren Najeriyar dai labarin wasannin na cewa, tsohon dan kwallon Super Eagles, Tijjani Babangida ya bukaci ‘yan wasan Da su yi amfani da bangaren dama da hagu na kungiyar inda nanne karfinta yake, watau Ahmed Musa da Moses sannan ya baiwa ‘yan wasan baya shawara da suma sai sun kula.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Ahir dinka, karka kara dangantamu da Peter Obi, Haramtacciyar kungiyar IPOB ta gargadi Kwankwaso

Leave a Reply

Your email address will not be published.