fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Labarin wasanni: Dani Alves zai koma Arsenal

Labarin wasanni na cewa tauraron dan kwallon kasar Brazil me bugawa kungiyar PSG wasa, Dani Alves zai koma Arsenal da buga wasa bayan da kwantirakin shi ya kare a PSG.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Labarin wasannin da AS ta ruwaito tace Manchester City da Tottenham suna neman Alves amma rahotanni sun bayyana cewa Arsenal ya zaba zaije.
Alves ya shirya rage albashinshi dan ya koma Arsenal, ya bukaci a rika biyanshi albashin fan dubu dari 200 maimakon fan dubu dari 230 da yake karba duk sati a PSG.
Dama dai Alves yayi aiki tare da kocin Arsenal din, Unai Emery lokacin yana PSG.
A wani labarin wasanni kuma da Daily Mail ta ruwaito, Manajan Gareth Bale ya karyata rade-radin dake yawo cewa dan wasan zai koma tsohuwar kungiyarshi ta Tottenham inda yace babu wannan magana a kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

Leave a Reply

Your email address will not be published.