fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Wannan hoton na shugaban kasar Koriya ta Arewa tare da yara ya dauki hankulan mutane

Shugaban kasar Koriya ta Arewa kenan Kim Jong Un a wani filin wasa zagaye da yara,  kamfanin dillanci labarai na Reuters ne ya wallafa wannan hoton inda yace shugaban kasar yana da wani abinda yake so(rauni) wanda watakila zai iya sa mahukuntan wasan Olympic su jawo ra’ayin kasar Koriya ta Arewar shiga wasannin na Olympic, yana san wasanni.

To saidai wadanda sukayi sharhi akan wannan hoto abubuwa biyune sukaja hankulansu:

Na daya mutane sun rika tambayar wai shin meyasa duka yaran dake cikin wannan hoto suke kuka, guda dayane kawai ke dariya? Wasu sun yiwa hakan fassara da cewa jin dadin ganin shugabanne kuma gashi kusa dasu har suna tabashi, wanda ba kowa bane yake samun wannan dama ba, shine ya sakasu kuka.

Karanta wannan  Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele, kuma DSS sun kamashi

Abu na biyu da aka rika barkwanci dashi akan wannan batu shine, wasu sun rika fada cikin barkwanci karfa aje a jawo kassr ta koriya ta Arewa cikin wasan Olympic din iidan tazo batayi nasara ba shugaban kasar yayi fushi ya kaiwa kasashe hari da makamin kare dangi na nokiliya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *