fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Labarin Wasanni:Lokacin da Ina Barcelona muka ci PSG 6-1 ne bazan taba mantawa dashiba>>Neymar

Tauraron dan kwallon kasar Brazil, Neymar dake bugawa kungiyar PSG ta kasar Faransa wasa wanda yake kokarin komawa tsohuwar kingiyarshi ta Barcelona an tambayeshi wane lokaci ne ba zai taba mantawa dashi a tarihin wasan kwallo da yayi? Amsar da ya bayar PSG ba zata ji dadinta ba, kamar yanda Labarin wasanni suka bayyana.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Labarin wasannin sun ci gaba da cewa, oh my goal sun tambayi Neymar wane lokaci ne ba zai tana mantawa dashi ba a harkar kwallo da yayi? 
Bayan yin tunani na dan lokaci sai ya kada baki yace, lokacin yana Barcelona, cin da sukawa PSG a gasar cin kofin Champions League na 6-1, ban taba jin farin ciki irin na wannan lokaci ba,injishi.
Da kuma aka tambayeshi wane lokacine ba zai manta dashi ba a dakin canja kaya na kwallo sai ya kara da cewa, ita dai wannan rana ce bazai manta da ita ba, dan kuwa bayan tashi daga wasan bayan sun koma dakin canja kaya sun yi murna sosai, kamar yanda labarin wasanni suka ruwaito.
Yau dai ake sa ran Neymar zai koma Faransa dan fara atisaye a PSG Gobe Litinin.
Dan wasan dai ba sai daya ba ya sha gayawa kungiyar cewa yana son barinta.
Saidai matsala daya da zai fuskanta wajan barin kungiyar shine kudin da suka sa mai na Miliyan 300 da duk kungiyar dake sonshi zata biya kamin su sayar dashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Kalidou Koulibaly da Raheem Sterling sun bugawa Chelsea wasan Premier league na farko da kafar dama

Leave a Reply

Your email address will not be published.