fbpx
Monday, August 8
Shadow

Lagos ta bayar da umarnin sakin mutane 253 da aka kama game da zanga-zangar #ENDSARS

Babban Lauyan Legas kuma Kwamishinan Shari’a, Moyosore Onigbanjo ya shawarci kotuna da su hanzarta sakin mutane 253 da ‘Yan sanda suka kama dangane da zanga-zangar #EndSARS a jihar.

Onigbanjo ya ce, Direktan Gabatar da Kara na Jihar (DPP) ya tantance tuhume-tuhume na dan lokaci da ‘yan sanda suka shigar a kansu kuma ba su samu wata shaidar farko ba ta cewa sun aikata wani laifi.
A cewar wata sanarwa daga Daraktan, Hulda da Jama’a a Ma’aikatar Shari’a, Kayode Oyekanmi, Babban Lauyan ya bayyana cewa ‘yan sanda sun gabatar da kararraki 40 game da mutane 361 da aka kama dangane da #EndSARS zuwa DPP don Neman Shawara, tsakanin Nuwamba 4 da 5, 2020.
Onigbanjo ya ce: “An bayar da shawarwari a kan doka game da dukkanin kararraki 40 da aka karba, kuma ya zuwa ranar 6 ga Nuwamba 2020, Daraktan ya bada Shawarwarin Shari’a game da mutum 81 da ake tuhuma zuwa kotuna daban-daban, yayin da wasu kuma za a tura su kotu ranar Litinin, 9 ga Nuwamba 2020.
Kuma ya tabbatar wa jama’a cewa “Ofishin Babban Lauyan na Jihar Legas zai tabbatar da cewa wadanda‘ yan sanda suka cafke ana bi da su kamar yadda doka ta tanada, yayin da ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da bin doka da kuma tabbatar da zaman lafiya da oda a cikin Jiha ”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Asiwaju Bola Ahmad Tinubu yace zai cigaba daga inda shugaba Buhari ya tsaya idan ya lashe zabe

Leave a Reply

Your email address will not be published.