fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Lai Mohammed ya bukaci a soke rajistar membobin APC a Jihar Kwara

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed a ranar Litinin ya yi kira da a hanzarta soke aikin rajistar mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke gudana a jihar Kwara.

Ministan ya ce an gudanar da atisayen ne ta hanyar zamba kuma ba tare da bin ka’idoji ba a jihar.

Ya bukaci Sakatariyar jam’iyyar ta kasa a maimakon haka, ta samar da wani tsari da zai tabbatar da gudanar da ingantaccen aiki wanda zai samu goyon baya da kwarin gwiwar kowa.

Lai Mohammed ya kuma yi kira da a gaggauta wargaza kwamitin rajistar membobin jihar karkashin jagorancin Sanata John Danboyi.

Ya kara da cewa mafi yawan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar basu aminta da kwamitin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *