fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Lai Muhammad ne babbar matsalar gwamnatin Buhari, duk abinda ya fada mutane na ganin karyce>>Kakakin APC

Mataimakin daraktan yada labarai na jam’iyyar APC,  Yekini Nabena ya caccaki Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad inda yace shine babbar matsalar gwamnatin shugaban kasa,Muhammadu Buhari.

 

Ya bayyana hakane a matsayin martani kan kiranshi da sunan sojan gona da Lai Muhammad din yayi. Lai Muhammad ya nemi da a soke sabunta rijistar APC da ake yi a jihar sa ta Kwara saboda yace ta sabawa dokar jam’iyyar.

 

Saidai a martanin Nabena yace Lai Muhammad ya gaza a gwamanatinsa, baya iya komai. Mutane ma da yayi magana suna ganin karyace kawai yace, yace in ba haka ba, ya fito ya fadi irin gudummawar da ya bada a gwamnatin shugaba Buhari

 

Yace a matsayinsa na Ministan yada labarai kamata yayi ace shine ke yiwa jama’a bayanin yanda tsarin gwamnati yake amma ya kasa. Yace tuni an bar Lai Muhammad a baya kuma idan yana zo ya dawo a tafi dashi to sai ya koma ya bi gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara dan su yi aiki tare.

 

“Lai Mohammed and his fifth columnists are the biggest problems of this administration. As the Minister of Information and Culture that suppose to explain the policies and programmes, including the remarkable achievements of this administration to Nigerians, Lai Muhammed has failed woefully. Whatever he says is considered a lie. If not, Lai should tell Nigerians what has been his contributions in the last five years.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *