fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Lalata suke yi damu suna suna bamu kwaya suna dukanmu kamar dabbobi, cewar matar da aka kaita kasar Mali don yin aiki mai tsoka

Wata mata mai suna Chinara ‘yar Najeriya ta bayyana irin wahalar data sha tare da abokanta a kasar Mali bayan an kaisu da nufin aiki mai tsoka.

Matar taje kasar ne bayan an ce mata zata samu aikin da za’a rika biyanta naira 150,000 a kowane wata, kuma dama iyayenta sun mutu gashi tanada yara uku da kannai hudu wanda duk nauyinsu ya rataya a wuyanta.

Saboda haka ne ta amince amma sai aka kaisu wani gida wanda ake yin lalata dasu ana basu kwaya tare da aikin wahala, kuma suna zane su kamar dabbobi.

Karanta wannan  Kalidou Koulibaly da Raheem Sterling sun bugawa Chelsea wasan Premier league na farko da kafar dama

Tace mata da dama sun mutu a gabanta, kuma tayi nasarar dawowa gida Najeriya ne bayan ta hadu da wani jami’in hukumar dake lura da shige da fice ta kasar Najeriya a Malin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.