Zakarun gasar Champions League Bayern Munich suna shirin aron tauraron dan wasan Chelsea Hudson Odoi har izuwa karshen wannan kakar tare da zabin siyen shi a farashin yuro miliyan 70 kaka mai zuwa.
An samu labari daga Sky Germany cikin wannan makon cewa da yiyuwar Bayern Munich ta siya Hudson Odoi bayan ta dade tana harin siyan dan wasan.
Munich ta dauki lokaci tana harin siyan dan wasan Ingilan mai shekaru 19 yayin da har ta mayar da shi babban dan wasan da zata siya a shekarar data gabata har ta taya shi a yuro miliyan 30, kuma Chelsea tayi burus da tayin munich na hudu data yiwa dan wasan na yuro miliyan 22.5 a 2019.
Odoi ya buga mintina 83 a wasan Chelsea na yau wanda ta lallasa Crystal Palace 4-0 kuma Frank Lampard ya bayyana cewa yana cikin tsarin shi a kungiyar amma ko a ranar litinin da za’a kulle kasuwa Munich zata iya siyan shi.