Wani bawan Allah daya ga wasu hotunan da aka dauka da hukumar gidan talabijin ta kasa watau NTA a takaice ke hira da wani farar fata da wata tsohuwar lasifikar magana ya wallafa hotunan a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda ya tambayi cewa wai duka-duka nawane lasifikar magana da bazaku iya siyaba?
Tun bayan da wannan bawan Allah ya wallafa wannan korafi nashi sai abin ja dauki hankalin mutane akayi ta nanatashi da dannan alamun sonshi, kai har ita kanta hukumar ta gidan talabijin ta kasa NTA din saida ta danna alamar cewa tana son wannan batu.
Wasu da sukayi sharhi akan wannan batu sunce sukam yanzu bama su kallon NTA din wasu kuwa cewa sukayi wannan abin kunyane kuma ma wai dan kasar wajene ake hira dashi, wai basa kallon yanda sauran gidajen talabijin suke da abubuwansu tsaf-tsaf?.