fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Lauya ya shawarci gwamanan jihar Osun Oyetola daya rungumi kaddara ya taya Adeleke murna kamar yadda shugaba Buhari yayi

Lauya Pelumi Olajengbesi ya shawarci gwaman jihar Osun Oyetola cewa ya rungumi kaddara kawai ya taya dan takarar PDP Adeleke murna kamar yadda shugaba Buhari yayi.

A yau hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana cewa Ademola Adeleke dan takarar PDP ne yayi nasarar lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar asabar.

Kuma mutane da dama sun taya shi murna musamman memebobin PDP hadda shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wanda hakan yasa lauya Pelumi Olajengbesi dan PDP ya shawarce shi daya bi sahun uban gidansa Buhari ya taya Adeleke murna domin zaiji kunya idan ya kai kara kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.